ABNA24 : Jaridar Ha’arez ta yahudawan ta bayyana cewa hukumar leken asiri ta cikin gida wato ‘Shabok’ ta kira wasu fitattun ‘yan siyasa masu goyon bayan kungiyar Hamas a yankin yamma da kogin Jordan inda ta ja kunnensu kan shiga zabubbukan Falasdinawa masu zuwa.
Labarin ya kara da cewa idan ‘yan siyasa masu goyon bayan Hamsa sun sami nasara a zabubbukan kamar yadda suka yi a shekara ta 2006 to yahudawan zasu dakatar da bawa gwamnatin Falasdinawan kudaden da take basu na haraji da na fito wanda kuma zai zama matsala ga biyan albashin ma’aika.
342/